Rundunar Sojojin Najeriya sun samu babban nasara ta fannin leken asiri da yakar masu miyagun manufa, bayan da suka kashe wani mai daukar hoto na kungiyar ISWAP a wani yunkurin kai hari da ya ci tura a garin Bitta, karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno.

Wata majiya ta tsaro ta shaida mana cewa dakarun sun dakile harin, tare da kwato wata na’urar daukar hoto mai inganci da ‘yan ta’addan suka yi niyya su yi amfani da ita wajen shirya bidiyon yada farfaganda.

Rahoton ya bayyana cewa mayakan ISWAP sun shirya harin ne domin su kirkiri bidiyon da zai tayar da hankalin al’umma, tare da kokarin nuna cewa suna da karfi da iko a yankin – duk da cewa an karya musu lagon.
A kashe dai an gano wani da ke a matsayin mai daukar hoto na kungiyar, kasancewar yana sanye da na’urar daukar hoto ta musamman da jakar kayan daukar bidiyo a jikinsa. An kashe shi ne a yayin musayar wuta da sojojin Najeriya.
A halin yanzu, bidiyon da na’urar dauka na hannun jami’an tsaro, inda ake ci gaba da nazarin ta domin fitar da bayanan sirri da za su taimaka a cigaba da fatattakar ‘yan ta’addan.