Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Mata ta Najeriya, Super Falcons, ta iso birnin Rabat na ƙasar Maroko domin buga wasan karshe na gasar 2024 Women’s Africa Cup of Nations (WAFCON) da za ta fafata a Atlas Lionesses na Maroko.

Ƙungiyar da Justine Madugu ke jagoranta za ta fara atisaye na farko a daren yau a cibiyar FUS Academie da ke Rabat, inda mintuna 15 din farko za a bawa manema labarai damar shiga.
Ana sa ran Super Falcons za su ci gaba da atisayen ba tare da manema labaran ba, kuma zasu ci gaba da wannan atisayen a wurin har zuwa gobe Juma’a domin kammala shirin su kafin wasan.
Najeriya za ta kece raini da Maroko a filin wasa na Olympic Stadium da ke Rabat a ranar Juma’a.
Super Falcons sun samu nasarar doke ƙungiyar Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu da ci 2-1 a wasan kusa da na ƙarshe da aka fafata a ranar Talata.
A nata ɓangaren, Maroko ta samu tikitin zuwa wasan ƙarshe ne bayan ta lallasa kungiyar kwallon kafar Mata ta Black Queens ta Ghana da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.