Rundunar ‘yan sanda a jihar Akwa Ibom ta kama wani mutum da ake zargin sa da kasancewa mamba na kungiyar asiri, tare da gano wasu kayayyaki da suka hada da Ƙoƙon kan bil adama a wurin sa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Timfon John, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, inda ta ce wanda ake zargin mai suna Pius Pius, baya ga kasancewarsa ɗan kungiyar asiri, ana zarginsa da aikata sata da lalata kayayyakin wutar lantarki a wasu sassan jihar.
An kama shi ne a ranar Lahadi a unguwar Oku Abak da ke karamar hukumar Abak.
“A yayin binciken da aka gudanar, Mr. Pius ya amsa cewa shi mamba ne na kungiyar asiri ta Iceland Confraternity, wadda ke da hannu wajen lalata muhimman kayayyakin gwamnati,” a cewar DSP John.
Ta kara da cewa bincike da aka gudanar a dakinsa ya haifar da gano wasu kayayyaki da suka hada da:
Ƙoƙon kan mutum
Na’urar sauya karfin wutar lantarki (transformer step-down insulator)
Na’urar dakatar da wuta (circuit breaker)
Mitar wuta (electric meter)
Da wasu fuyus-fuyus na lantarki (fuses).
DSP John ta ce bincike na ci gaba da gudana, tare da shirin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala