Rasha ta kaddamar da sabbin hare-hare ta amfani da jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami a sassa daban-daban na Ukraine da safiyar yau, kwanaki bayan Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya nemi a gudanar da sabon zagaye na tattaunawar zaman lafiya.

Duk da wannan kira na sulhu, birnin Moscow bai mayar da martani ba har zuwa wannan lokaci, sannan ba ta mayar da martani kan barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi ba — inda ya ce za a samu ci gaba da tattauna yarjejeniyar zaman lafiya ko kuma Rasha ta fuskanci takunkumi masu tsanani.
Zelensky ya bayyana cewa mutane biyu sun mutu, yayin da akalla 15 suka jikkata a hare-haren da aka kai, ciki har da yaro dan shekara 12. Kan ya bayyana harin a matsayin “hari ne kan bil’adama”, yana mai ƙara jaddada bukatar tallafi da tallafawar duniya kan abinda ke faruwa a ƙasarsa.
Hare-haren na yau na zuwa ne a daidai lokacin da Ukraine ke ƙara matsin lamba kan ƙasashen duniya su taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin da ya haura shekaru biyu, tare da bayyana matsalolin da ƙasar ke fuskanta sakamakon ci gaba da luguden wuta daga Rasha.