Wata gobara da ta tashi a masana’antar Shril-Balaj Industrial Limited da ke unguwar Olopomeji, a garin Ibadan, jihar Oyo, ta yi sanadin asarar dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin nairori, a cewar hukumomi.

Lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi, inda sashen ajiye tsofaffin kayan da ake amfani da su wajen sarrafa kayayyaki, musamman tayin motoci, ya fi shan barna.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta fara ne daga wannan sashen da ke ɗauke da tarin tsofaffin tayoyi, kafin ta bazu zuwa wasu sassa na masana’antar, lamarin da ya haifar da gagarumar asara.
Shugaban Hukumar Kula da Gobara ta Jihar Oyo, Maroof Akinwande, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar. Ya ce sun samu kiran gaggawa kan tashin gobarar da misalin karfe 7:07 na safe a ranar Lahadi.
Akinwande ya bayyana cewa jami’an hukumar sun gaggauta zuwa wajen da lamarin ya faru domin shawo kan gobarar, tare da dakile yaduwarta zuwa wasu sassa na masana’antar da ke makwabtaka.
Yayin da ba a riga an tantance musabbabin tashin gobarar ba, hukumomi sun ce bincike na ci gaba da gudana domin gano asalin dalilin aukuwar lamarin.