Rahotanni daga kasuwanni daban-daban sun nuna cewa farashin buhun takin urea ya karu daga tsakanin N35,000 zuwa N37,000 da ake sayarwa a baya-bayan nan, zuwa tsakanin N47,000 da N50,000 a yanzu.

Haka zalika, farashin buhun takin NPK a mafi yawan ƙauyuka yana kaiwa tsakanin N48,000 zuwa N55,000, abinda ke ƙara tsananta damuwar manoma da masu ruwa da tsaki a fannin noma.
Shugaban ƙungiyar manoman Najeriya (AFAN), Arc. Kabiru Ibrahim, ya bayyana cewa wannan lamari babban barazana ne ga burin ƙasar na cimma isasshen samar da abinci. Ya ce tsadar taki na iya sa manoma rage yawan abin da za su noma ko kuma su daina gaba ɗaya, lamarin da zai ƙara haifar da ƙarancin abinci da tashin farashin kayan masarufi.
Kabiru Ibrahim ya bukaci gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa wajen tallafawa manoma da rage farashin taki, domin ceto Najeriya daga wata gagarumar matsalar abinci da ka iya shafar rayuwar al’umma da tattalin arzikin ƙasa.