Mai horas da ƙungiyar mata ta Afirka ta Kudu, Banyana Banyana, Desiree Ellis, ta bayyana damuwa kan gajiyar da ta bayyana a jikin ‘yan wasanta, kafin karawar su da Super Falcons ta Najeriya a wasan kusa da na ƙarshe na Gasar Cin Kofin Mata ta Afirka (WAFCON).

Za a buga wasan ne a ranar Talata a filin wasa na Stade Larbi Zaouli da ke Casablanca, a ƙasar Morocco.
Afirka ta Kudu, wadda ke rike da kambun gasar, ta sha wahala kafin ta doke Senegal a zagaye na baya ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron raga (penalty shootout), domin samun damar tsallakewa zuwa zagaye na gaba.
Kocin Ellis ta bayyana cewa irin ƙarfin da ‘yan wasan suka yi amfani da shi wajen doke Senegal na iya shafar kuzarin su a wasan gaba da Super Falcons.
Super Falcons kuwa za su shiga wannan wasa da kwarin gwiwa, bayan da suka doke Copper Queens na Zambia da ci 5-0 a wasan da aka buga a ranar Juma’a da ta gabata.
Yanzu haka, ana sa ran fafatawar za ta kasance mai zafi, ganin cewa dukkan ƙasashen biyu na daga cikin manyan ƙungiyoyin mata a nahiyar Afirka.