Jam’iyyar ADC ta soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa gazawarta na naɗa sabbin jakadu, fiye da shekara guda bayan ta janye dukkan wakilan diflomasiyya 109 na Najeriya daga ƙasashen waje.

A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a ranar Lahadi, ADC ta bayyana jinkirin a matsayin “Koma baya ga martabar diflomasiyyar Najeriya” wanda ya rage ƙimar ƙasar a idon duniya tare da barin ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje cikin hali na rashin samun cikakkiyar kariya ta diplomaciyya.
SKM HAUSA ta ruwaito cewa a watan Satumban 2023 ne Shugaba Tinubu ya janye dukkan jakadun Najeriya, ciki har da jami’an diflomasiyya 41 da ake kira da non-career, da kuma jakadun diflomasiyya 42, ba tare da bayyana dalili ba.
Tun daga wannan lokacin Najeriya bata da wakilci na jakadu a ƙasashe da dama, domin babu sabbin naɗe-naɗe da aka sanar.
A halin yanzu, jakadun wucin gadi da ma’aikatan ofisoshin jakadanci irinsu chargés d’affaires da consuls-general ke ci gaba da gudanar da ayyukan diflomasiyya, duk da cewa ba su da cikakken iko da damar shiga manyan tattaunawa, wakilcin siyasa ko halartar tarukan diflomasiyya na matakin ƙasa da ƙasa .
A cewar ADC, wannan gibi yana da “illoli masu tarin yawan,” ciki har da matsalar da ake fuskanta a halin yanzu kan batun biza da sauran ayyukan jakadanci da ƙasashe kamar Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa.
“Jakadu na wucin gadi ko ƙananan ma’aikatan diflomasiyya ba za su iya maye gurbin jakadu na dindindin ba,” in ji ADC. “Irin waɗannan ba su da cikakken iko da girmamawa da ake buƙata don kare muradun Najeriya.”
Jam’iyyar ta kuma yi gargaɗi cewa idan gwamnatin Tinubu ta ci gaba da yin jinkiri wajen naɗa sabbin jakadu, akwai yuwuwar wasu ƙasashe su rage matakin wakilcinsu a Najeriya zuwa ƙananan ma’aikata kamar chargés d’affaires.