Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin, ta ƙi amincewa da buƙatar tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, na a mayar masa da fasfo ɗinsa domin tafiya ƙasar Birtaniya don neman lafiya.

Mai shari’a Emeka Nwite, wanda ke sauraron shari’ar zargin almundahanar kuɗi da ya kai Naira biliyan 80 da ake yi wa Yahaya Bello, ya yanke hukuncin cewa bai kawo hujjoji masu ƙarfi da za su tabbatar da sahihancin buƙatarsa ta zuwa neman lafiya ba.
Wannan hukunci ya biyo bayan irin wannan mataki da wani alkalin babbar kotun birnin tarayya (FCT) ya ɗauka kwanaki kaɗan da suka wuce, inda kotun ta kuma ƙi amincewa da buƙatar Yahaya Bello na tafiya waje don lafiya, duk da cewa yana fuskantar tuhuma kan zargin almundahanar kudi da ya kai Naira biliyan 110 a wannan kotu.
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa EFCC ce ke gurfanar da Yahaya Bello a gaban duka kotunan biyu, kuma ta nuna adawarta da buƙatun nasa a yayin zaman kotu daban-daban. EFCC ta bayyana cewa akwai yiwuwar Bello ya tsere, musamman ganin yadda ya ƙi bayyana a kotu sau da dama duk da samun sammacin gurfana, kafin daga bisani ya mika kansa bayan watanni.