 
        Tsagerun sun dauki hanyar hana gudanar da karatu domin kuwa sun shiga cikin dare sama da su 30 inda suka cire kofofin makarantar da tagogi da dukanin Wani Abu Mai amfani a makarantun
Guda cikin tsofafin daliban makaranta Bashir sharif Ibrahim yace lamarin ya Basu mamaki yadda matasan suka rushe makaratan primary ta zawa’i kafin shigowa wadanan makarantu
Sai dai shugaban hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar kano Rabiu sale Gwarzo ya ce, sun samu labarin faruwar lamarin Kuma tuni suka dauki matakin kawo masu Gadi domin hana batagari cigaba da kwashe Mayan makarantar
Sai dai rahoton da Skm hausa ta samu ya bayyana cewa tuni matasan sun yiwa makarantar karkaf, inda hatta masallacin makarantar basu bari ba.
A wani labarin makamancin wannan yanzu haka dai matasan sun rushe makarantar primary ta zawa’i tare da siyar da bulon Ginin akan naira dari biyu 200.
Barazanar fadan daba dai na ci gaba da jefa fargaba a zukatan al’umma lamarin da ya kamata gwamnati da al’umma su yi karatun ta nutsu.
 
         
         
         
         
        