Wani mummunan haɗarin mota ya hallaka sama da mutane 20 a garin Dakatsalle dake yankin karamar hukumar Garin Malam.
Kakakin hukumar kashe gobara a jihar Kano Saminu Yusuf ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce haɗrin ya wanzu ne tsakanin wata mota ƙirar hoho da kuma motar Bus wato homa insa suka yi taho mu gama, inda a nan ne motocin suka kama da wuta.
Hadarin dai ya shafi kimanin mutane 28 inda 3 daga ciki ne kaɗai suka tsira da rayuwar su, inda 25 daga cikinsu suka ƙone sakamakon hadarin.
Motar Bus din dai tana kan hanyar ta ne daga kudancin Nigeria zuwa jihar Kano inda take ɗuke da mutane sama da 20, yayin da motar dakon kayan kuma ke dauke da mutane 7 inda take dauke da nau’in kayan abinci.
Hadari ta ce musabbabin haɗari shi ne aron hannu da mai motar kirar homa buss yayi.