Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya shi ne ya hana a kashe jagoran juyin juya halin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a lokacin rikicin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila, yana mai zargin Khamenei da rashin nuna godiya.
A cikin wani saƙo mai zafi da ya wallafa a dandalinsa na Truth Social, Trump ya caccaki Iran bisa ikirarin cewa ta yi nasara a yaƙinta da Isra’ila da kuma cewa harin jiragen Amurka bai janyo mata babbar barna ba.
Shugaban ya bayyana cewa shi ne ya dakatar da duk wani yunkuri na sassauta takunkumi da aka sanya wa Iran saboda rashin jin daɗin kalaman Khamenei.
Trump ya ƙara da cewa zai sake umartar kai harin jiragen yaƙi idan Iran ta ci gaba da ƙoƙarin kera makamin nukiliya, yana mai cewa: “Za mu sake kai hari ba tare da tantama ba idan har suka ci gaba da ganin suna daikon ƙera makamin nukiliya.
”Game da Khamenei, Trump ya rubuta cewa:“Na san inda ya buya sosai, kuma ban yarda Isra’ila ko dakarun Amurka su kashe shi ba, duk da ƙarfinmu. Na cetoshi daga mutuwa mai muni da wulakanci — kuma bai ce, ‘Na gode Shugaba Trump!’ ba.”
Trump ya bayyana cewa ya kusa cimma matsaya kan sassauta takunkumi, amma bayan kalaman da Khamenei ya fitar, sai ya dakatar da duk wani shiri. “Ina fata Iran za ta dawo teburin tattaunawa,” in ji Trump.
Sai dai Iran ta musanta cewa tana shirin komawa tattaunawa da Amurka, kamar yadda Trump ya bayyana a taron NATO da aka yi a birnin The Hague.
Ministan harkokin wajen Iran ya ce babu wani sabon shiri na tattaunawa, yana mai kore zancen da Trump ya yi.
