
Daga Saifullahi Gambo Minjibir
A zantawarsa da Skmhausa shugaban ƙaramar hukumar Hon Jibrin Nalado Alliyu ya bayyana cewa kasafin kudin na wannan shekarar ya tasamma naira Biliyan 10, wanda fannin ilimi zai samu kaso mai tsoka.
Kaso na biyu da zai samu kaso mai tsoka a kasafin kuɗin shi ne fannin lafiya, domin tabbatar da magance matsalolin dake addabar Asibiticin yankin.
Abu na uku da kasafin zai kunsa shi ne fannin samar da ruwan sha, la’akari da yadda ake fuskantar matsalar ruwa a ƙaramar hukumar Minjibir.Shugaban Hon Jibrin Nalado Aliyu ya kara da cewa kaso na huɗu a kasafin kudin shi ne samar da yanayi mai kyau a lungu da saƙo na karamr hukumar.
Zalika shugaban ya bayyana bangaren ayyukan yau da kullum zai lashe kaso 70 na kasafin kuɗin wannan shekara.Al’umma da dama ne dai suka halarci taron waɗanda suka haɗar da shugabannin gargajiya, kungiyoyin al’umma daga mazaɓu 11 dake faɗin ƙaramar hukumar ta Minjibir.
A karshe shugaban ya buƙaci Al’ummar yankin su bawa gwamnati hadin kai da goyon baya domin samun ɗorewar ayyukan raya ƙasa a yankin.