Minna, Neja – Akalla mutane 29 sun rasa rayukansu a wani sabon hatsarin jirgin ruwa da ya auku a kauyen Gausawa na unguwar Malale, karamar hukumar Borgu a jihar Neja.

Daraktan hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba-Arah, ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Minna a ranar Laraba.
A cewar Baba-Arah, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar Talata, lokacin da jirgin ruwan ya taso daga Tungan Sule a unguwar Shagunu dauke da fasinjoji 90, ciki har da Mata da yara, inda suke kan hanyarsu zuwa Dugga domin yin ta’aziyya.
Ya ce jirgin ruwan ya ci karo da wani itacen da ke tsakiyar ruwa, lamarin da ya janyo mummunan hatsarin.
Shugaban na (NSEMA) ya ce an gano gawarwakin mutane 29, yayin da aka ceto mutane 50 da ransu, sai kuma mutum biyu da ake ci gaba da nema.
Ya kara da cewa binciken farko ya nuna yawan fasinjojin da kuma haduwar jirgin da itacen ne suka jawo aukuwar hatsarin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan shi ne karo na biyu da irin wannan mummunan hatsari ya auku a jihar Neja cikin ‘yan watannin nan. A watan Yuli da ya gabata ma, wani hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 25, ciki har da mutane 10 daga iyali guda.