Ado Danladi Farin Gida- Kano
Wata kotu a jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Yusuf Ishak hukuncin daurin sati biyu a gidan gyara hali da tarbiyya, tare da umartar sa da rubuta takardar neman afuwa ga hukumar kwashe shara ta jihar Kano.

An gurfanar da Yusuf a gaban Kotun Majistire mai lamba 7, bisa tuhume-tuhume da suka haɗa da zubar da shara a kusa da gadar Dangi da ke kan titin Kano–Zariya, da kuma hana ma’aikatan hukumar yin aikinsu tare da cin zarafinsu.
Bayan karanta masa tuhume-tuhume, Yusuf ya amsa laifinsa. Daga nan ne mai shari’a Halima Wali ta yanke masa hukuncin daurin sati biyu a gidan gyara hali da tarbiyya ko biyan tarar ₦15,000.
Bayan kammala zaman kotun, shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano kuma shugaban kula da tsaftar muhalli, Dr. Muhammad S. Khalid, ya bayyana irin dokokin da Yusuf ya karya, ciki har da ɓata muhalli ta hanyar zubar da shara a titi da kuma cin zarafin ma’aikaci. Ya ce matashin ya yi barazanar sake zuwa hukumar domin zubar da shara a gaban jami’ai.
Daga nan sai shugaban hukumar ya yi gargadi ga jama’a cewa hukumar ba za ta yi shiru kan masu karya doka ba, inda ya ce:
“Za mu fito da kotun tafi-da-gidan-ka domin hukunta duk wanda aka samu da laifin zubar da shara a tituna da unguwanni.”