
Wannan dai shi ne karo na uku da shugaban ƙaramar hukumar ta Minjibir karo na uku shugaban karamar, Capt JIBRIN NALADO ALIYU KUNYA ke rabo kujerun ga makarantun yankin domin farfaɗo da fannin ilimi.
A wannan karon shugaban ƙaramar hukumar ya raba Kujerun zama kimanin 500 ga makarantun primary, junior a fadin karamar hukumar.

Kawo yanzu Hon JIBRIN NALADO ALIYU ya raba kujeru sama da 2000 ga makarantun yankin wanda zai bawa Ɗalibai sama da 8,000, zama a kan Kujerun a yunkuri na kawo karshen zaman da Ɗalibai ke yi a ƙasa a fadin karamar hukumar ta Minjibir.
Capt. Jibrin Nalado Alliyu ya shidawa wakilinmu cewa ya samu damar gudanar da wannan aiki ne bisa sahalewar Gwamna Engr Abba Kabir Yusuf.
 
         
         
         
         
        