Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya nada Injiniya Abdurrazaq Abubakar Nakore a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na Jami’ar Ilimi ta Tarayya wato Yusuf Maitama Sule, dake Kano.
Injiniya Nakore, wanda ƙwararren injiniya ne, ya taba rike mukamin Sakataren Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara a Jihar Jigawa.
Haka zalika, shugaban kasar ya tabbatar da nadin Farfesa Abdullahi Tukur Kodage a matsayin Shugaban Jami’a (Vice Chancellor) na jami’ar ta tarayya dake Kano.
A wani bangaren kuma Shugaba Tinubu ya kuma amince da nadin Farfesa Yahaya Isa Bunkure a matsayin Shugaban Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Zariya, a Jihar Kaduna.
Farfesa Bunkure, wanda kwararre ne a fannin ilimin kimiyya, shi ne tsohon Shugaban Jami’ar Sa’adatu Rimi University of Education, Kano, kafin gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Engr Abba Kabir Yusuf ya mayar da ita gurbinta na asali wato College of Education.