Hukumar kula da madatsun ruwa ta Hadejia–Jama’are ta yi kira ga manoma masu amfani da ruwa da su guji almubazzaranci, tare da tabbatar da adalci wajen rarraba shi, domin kare muradun al’umma baki ɗaya.

Shugaban sashin injiniyanci na hukumar, Sani Yakubu Danladi, wanda ya wakilci manajan ayyuka a hukumar, Yakubu Sani,ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da sababbin shugabannin ƙungiyar manoma masu amfani da ruwa a jihar Kano.
A cewarsa, ruwan da ake samu daga madatsar ruwa ana turawa ne zuwa manyan koguna, inda kuma ƙungiyar manoma ke da hakkin rarraba shi ga ’yan uwa manoma.
A nasa jawabin, sabon shugaban ƙungiyar, Mustapha Adamu Mudawa, ya ce tsarin zaben shugabanni ana gudanar da shi duk bayan shekaru huɗu, kuma a bana aka ba su amanar jagoranci saboda irin jajircewa da nuna kishin manoma da suka yi.
Ya sha alwashin ganin cewa babu manomi da zai koka kan rashin ruwa a gonarsa, yana mai cewa:
“Za mu tabbatar da an rika rarraba ruwa da adalci da gaskiya domin amfanin kowa da kowa. Ruwa amana ce, kuma za mu yi aiki tukuru wajen ganin duk manomi ya ci gajiyarsa.”