
Wata Kotun A Finland Ta Yanke Wa Simon Ekpa Hukuncin Shekaru Shida a Gidan Yarin Ƙasar.
Kotun ƙasar Finland ta yanke wa Simon Ekpa, wanda ya ke kira kansa wanda ke kiran kansa da “Firaministan Biafra”, hukuncin shekaru shida a gidan yari bisa laifukan ta’addanci da kuma kin biyan haraji.
Kotun ta tabbatar da cewa Ekpa ya aikata laifin tayar da zaune tsaye a Najeriya, tare tallafa wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da makamai, baya ga amfani da kafafen sada zumunta wajen gudanar da ayyukan IPOB da ESN.
Idan za a iya tuna an kama shi ne a watan Nuwamba 2024, inda aka gurfanar da shi a kotu a watan Disamba 2024, sannan aka yanke masa hukunci a watan Agusta 2025.
Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro, musamman Hedkwatar Tsaro da kuma Hukumar DSS ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar Adeola Oluwatosin Ajayi, sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin an hukunta Ekpa.
To sai dai wasu ɓangare na al’umma a Najeriya na ganin cewa hukuncin ya yi sauƙi idan aka yi la’akari da irin zarge-zargen da aka yi wa Ekpa.
Yayin da masu sharhi kan lamuran tsaro ke ganin hukuncin zai zama darasi ga sauran masu shiga harkar ta’addaci.