Hadaddiyar kungiyar shugabannin makarantun Shari’a (Legal) ta Najeriya ta zabi Farfesa Abubakar Jakada a matsayin sabon shugabanta na kasa.

Wannan nadi ya biyo bayan taron da kungiyar ta gabatar a ranar Litinin 25/ 08/ 2025, wadda aka gabatar a kwalejin shari’a da addinin Musulunchi ta Malam Aminu Kano wato Legal.
Da yake karin haske kan wannan mukami da Farfesa Jakada ya samu, mai magana da yawun kwalejin ta Legal, Dr Salisu Marafa Sagagi ya bayyana cewa zaben ya biyo bayan amincewa da yarda da dukkanin mambobin kungiyar su ka yi.
Sannan ya ce zaben ya zama irin sa na farko da kwalejin Legal ta rabauta da shi tun bayan kafuwar kungiyar shekaru ashirin da uku da suka wuce.
Da yake mika sakonsa na godiya bisa wannan matsayi, Jakada ya gode wa yayan kungiyar bisa nuna goyon da amincewarsu a kansa, inda ya ce zai yi dukkan mai yiwuwa domin samun nasarar kungiyar da makarantu da suke wakilta.