Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Wakilai da ke binciken bashin Naira biliyan 59 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar domin shirin samar da mitocin wutar lantarki, ya nemi cikakken bayani daga Hukumar Kula da Harkokin Lantarki ta Ƙasa (NERC).

Kwamitin ya kuma tuhumi wasu kamfanoni bisa amincewa da wani kamfani na karɓar kashi 0.5% na kudaden shiga na shekara daga masu rarraba wutar lantarki har zuwa shekarar 2030.
Shugaban Kwamitin, Hon. Uchenna Okonkwo, ya bayyana cewa shirin an tsara shi ne domin toshe gibin mitoci, bunkasa samar da kayan aikin cikin gida, da kuma kawo ƙarshen matsalar rashin na’urorin mita a gidaje.
Sai dai, ‘yan majalisar sun nuna damuwa cewa duk da amincewar da aka yi tun shekarar 2020, shirin bai kawo sakamakon da ake sa ran gani ba.