
Rundunar Yan sandan Kano ta fitar da sabuwar sanarwa.A sanarwar da rundunar ta fitar kan zaɓukan cike gurbi da za’ayi a kananan hukumomin Ghari, Tsayawa, Sha’anin, da Ɓagwai wanda zai gudana a Asabar ɗin nan.
Rundunar ta bakin kakakin ta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta buƙaci, ƴan asalin waɗannan kananan hukumomin da za a gudanar da zaɓen su tabbatar su bi ka’idar da hukumar zaɓe ta gindaya.
Kazalika rundunar ta gargadi masu kada kuri’a su guji zuwa filin zaɓe da wani launin kaya da zai nuna tambarin jam’iyya.
Kiyawa ya kara da cewa rundunar bata yarda da aikin jami’an tsaron jihar Kano ba, kamar Karota, Vigilant da sauransu.Kazalika rundunar ta bayyana cewa ta sanya dokar takaita zirga-zirga a kananan hukumomin daga karfe 6:00-12 daran ranar Asabar.