Daga Wakilinmu – Ado Danladi Farin Gida, Kano
A wani mataki na kare muhalli da dakile barazanar kwararowar hamada, Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da shirin dashen bishiyoyi miliyan biyar da dubu dari biyar (5,500,000), wanda aka fara a garin Ɗan Bawa, cikin karamar hukumar Makoda.

Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya jagoranci kaddamarwar, inda ya bayyana cewa shirin zai shafi dukkan kananan hukumomi 44 na jihar. A cewarsa, “Za a raba bishiyoyin ne kyauta ga jama’a, makarantu, masallatai, ofisoshin gwamnati da gidajen mutane domin kara wayar da kai da kuma bunkasa yanayin muhallinmu.”
Shirin dai na zuwa ne a daidai lokacin da jihar ke fama da matsalar sauyin yanayi da kuma rashin isassun bishiyoyi da ke takura ci gaban muhalli mai dorewa.
Gwamna Abba Kabir ya bayyana jin dadinsa da kokarin da Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahiru Hashim, ke yi wajen tsara shirye-shiryen da ke amfanar muhalli da lafiyar al’umma.
“Wannan mataki ne muhimmi wajen kare rayuwar al’umma da tsare makomar muhallinmu,” in ji gwamnan.
A nata bangare, masarautar Kano ta goyi bayan shirin, inda Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ta bakin wakilinsa, Hakimin Gwarzo, Alhaji Bello Abubakar, ya bukaci gwamnati ta dawo da dokar hana sare bishiyoyi. Ya ce, “Kare bishiyoyi na da muhimmanci fiye da yadda ake dauka. Yana da nasaba da rayuwa kai tsaye.”