
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki Shugaban Bola Tinubu saboda rashin kai ziyara garin Yelewata a Jihar Benue, bayan harin kisan gillar da aka yi a yankin.
Shugaba Tinubu ya ziyarci Benue a ranar Laraba domin jajanta wa waɗanda harin ya rutsa da su, amma ya ce ba zai samu damar zuwa garin Yelewata ba saboda yanayin ruwan sama da ambaliya da kuma yadda hanyoyin yankin suka lalace.
Sai dai a cikin wata sanarwa da Peter Obi ya wallafa a shafinsa na X a yau Juma’a, ya ce shugabanci na buƙatar sadaukarwa a kowane lokaci, yana mai cewa mutanen Benue ba su buƙatar bayani, illa samun kulawa da jagoranci na gaskiya.
Obi ya ce ko da yake ba ya goyon bayan a jefa shugaban ƙasa cikin haɗari, hujjar da Tinubu ya bayar ba ta gamsar da shi ba, yana mai jaddada cewa gwamnatin tarayya da ta jiha ne ke da alhakin gyara hanyoyin da suka lalace.