
Rundunar tsaro ta musamman da gwamna Uba Sani ya kafa domin yaki da miyagun kungiyoyi masu aikata lefuka da masu satar wayoyin hannu, ta kama mutane 398 tare da kwato makamai a sassa daban-daban.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar DSP Hassan Mansir ya fitar, ta bayyana cewa sumamen sun samo asali ne daga sahihan bayanan sirri da aka samu, lamarin da ya sa da dama daga cikin masu aikata laifin suka tsere daga jihar Kaduna saboda fargabar kama su.
DSP Mansir ya ce an kama wani mai suna Adamu Umar, wanda aka dade ana zarginsa da safarar miyagun kwayoyi, tare da kwato bindiga kirar gida a hannunsa.
Yanzu haka an mika shari’arsa a hannun hukumar NDLEA domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi gaban Kotu.Haka kuma, sumamen ya haifar da kwato makamai masu hadarin gaske tare da miyagun kwayoyi da kuma wayoyin hannu 29 da aka sata. Daga ciki, an mayar da wasu ga masu su na asali bayan tantancewa da tabbatar da cewar mallakinsu ne.