
Harin ƴan Ta’adda Ya Rutsa da Jerin Motocin Ɗaukar Mai a Hanyar Kayes zuwa BamakoWasu da ake zargin ƴan ta’adda ne sun kai hari a kan jerin motocin ɗaukar mai a kan babbar hanyar Kayes zuwa Bamako a Mali, a ranar Lahadi.
Shaidu sun ce jerin motocin, wanda ake ganin shi ne mafi tsawo a tarihin kasar, ya gamu da maharan ne ba zato, lamarin da ya sa sojojin da ke rakiya suka janye daga wurin.An bar wasu tankunan mai a kan hanya, yayin da rahotanni suka ce wasu direbobi sun jikkata.
Lamarin ya jefa sakku ga al’umma, inda jama’ar ƙasar ke jefa alamar tambaya kan cewa duk da jiragen yaki, jirage masu saukar ungulu, motocin masu ɗauke da sulke da makamai masu nauyi, amma rundunar sojin Mali ta kasa dakile maharan da ke amfani da babura da bindigogin AK-47.
To sai dai har yanzu hukumomi ba su fitar da sanarwa game da adadin mutanen da suka mutu ko asarar dukiyar da aka yi ba.Masana tsaro sun bayyana cewa harin na nuna ci gaba da barazanar da ƙungiyoyin jihadi ke haifarwa a Mali, duk da dogon lokaci da aka shafe ana gudanar da hare-haren soji da kuma kuɗaɗen da aka zuba wajen tsaro.