
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tura sunayen mutum biyu zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatarwa a matsayin kwamishinoni a majalisar zartarwar jihar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Asabar.
An bayyana waɗanda aka nada a matsayin Barrister Abdulkarim Kabir Maude, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Minjibir, da kuma Dr. Aliyu Isa Aliyu, Farfesa mai taimako a fannin lissafi.
Tarihin Barr. Abdulkarim Kabir
MaudeBarrister Maude, mai shekara 40, ƙwararren lauya ne mai tasowa wanda zai karɓi lambar girmamawa ta Senior Advocate of Nigeria (SAN) a kotun koli gobe.Ya kammala karatun digiri na farko (LLB) a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, sannan ya samu BL a Makarantar Shari’a ta Najeriya da ke Abuja. Haka kuma, yana da digiri na biyu a fannin Dokar Tattalin Arzikin Ƙasa da Ƙasa, wanda yayi a Maryam Abacha American University of Niger, da kuma Master’s a fannin Business Commercial Law daga Jami’ar Bayero Kano.
Zalika ya yi aiki fiye da shekara goma a aikace, ya riƙe shugabancin ofishin lauya a Kano, tare da gogewa a fannin shari’a, gudanarw, da sauransu.
Tarihin Dr. Aliyu Isa Aliyu.
Shi kuwa Dr. Aliyu, mai shekara 41, ya kware a fannin lissafi tare da gogewa ta ilimi da gudanarwa. Ya samu digiri na farko daga Jami’ar Bayero Kano, digiri na biyu daga Jordan University of Science and Technology, sannan digirin digirgir (PhD) daga Firat University da ke Turkiyya.Ya fara aikin koyarwa a Jami’ar Tarayya Dutse tun daga shekarar 2014, inda daga baya ya zama Farfesa mai taimako a North West University, Kano. Haka kuma, ya yi bincike a matsayin Postdoctoral Fellow a Sun Yat-Sen University, China, da kuma Associate Adjunct Researcher a Near East University, Cyprus.
Tun daga shekarar 2023, yana rike da mukamin Babban Jami’in Kididdiga na Jihar Kano. An bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan masana lissafi a duniya, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka ci moriyar tallafin karatu na Kwankwasiyya.
Sabon Solicitor GeneralA wani ɓangare na sauyin, Gwamna Yusuf ya amince da naɗin Barrister Salisu Muhammad Tahir a matsayin sabon Solicitor General da Babban Sakatare na Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano.Kafin wannan mukami, Barrister Tahir shi ne Daraktan Hukunce-hukunce a ma’aikatar, inda ya yi fice wajen gudanar da ayyuka.
An umarci Shugaban Ma’aikata na Jihar Kano da ya kammala dukkan matakan gudanarwa don fara aikinsa daga Litinin, 29 ga Satumba, 2025.
Da yake tsokaci kan naɗin, Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na cusa nagarta, ƙwarewa da gaskiya a cikin hidimar gwamnati tare da shigar da sabbin matasa masu kuzari a cikin majalisar zartarwa.