Majalisar Malaman Musulunci ta Jihar Taraba, tare da hadin gwiwar shugabannin gargajiya da hukumomi, ta haramta gudanar da wasu bukukuwan da ke da alaka da bikin aure a garin Jalingo.

Shagulgulan da aka hana sun hada da ranar Kauyawa da Ajo, inda matasa maza da mata ke sanya kaya na musamman suna rawa daga yamma har zuwa dare, da sunan bikin aure.
Haramcin ya kasance jigon hudubar Juma’a ga dukkanin limaman masallatai a birnin Jalingo, inda aka gabatar da shi a ranar Juma’ar da ta gabata.