
Rundunar ƴansandan jihar Kano ta sanar da kama wani mutum ɗan shekaru 45.Rundunar ta bakin kakakin ta SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, sanyi nasarar kama Dahiru Jibrin ne a unguwar Sharaɗa.
Tunda fari dai wanda ake zargin wato Ɗahiru Jibrin ya je wajen wani bakaniken Babur inda ya bukaci ya samo masa babur mai kyau domin ya siya.
Inda a nan ne Bakaniken ya garzaya kasuwar Wapa ya kawo masa Mashin kirar Suzuki, inda a nan ne Ɗahiru ya cika wandonsa da iska.Yanzu haka dai Rundunar ta tabbatar da samo wancan Bubur da Ɗahiru ya sace.
Kakakin rundunar ta ƴansandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bukaci duk wanda yasan an sace masa Bubur to ya garzaya zuwa shalkwatar rundunar ƴansandan wato Bompai domin karin bayani.